2015: APC ta dauki hayar kamfanin Amurka

Image caption Shugaban jam'iyyar APC, Bisi Akande

Babbar jam'iyyar adawa ta APC a Nigeria ta sanarda daukar hayar wani babban kamfani mai suna AKPD da ya kware wajen taimakawa 'yan siyasa lashe zabuka.

A wata sanarwa, kakakin APC Alhaji Lai Muhammed ya ce APC ta kulla yarjejeniya da kamfanin AKPD na Amurka don taimakawa jam'iyyar da dabarun lashe zabukan 2015.

Kamfanin AKPD ya taimakawa Shugaban Amurka, Barack Obama wajen lashe zabe a shekara ta 2008 da kuma 2012.

Jam'iyyar APC ta ce kamfanin ya yi aiki tare da wasu gaggan 'yan siyasa a Amurka wadanda suka samu nasara a zabe.

Kamfanin AKPD ya taka rawa wajen samun nasarar 'yan siyasa a kasashen Kenya da Tanzania da kuma Ghana.

Karin bayani