Rikicin masu neman mafaka a Australia

Image caption Sansanin masu neman mafaka da ke tsibirin Manus.

An kashe wani mai neman mafaka a Australia tare da jikkata wasu mutanen 77 a dare na biyu na hatsaniyar da ta barke a wani sansanin tsaron masu neman mafaka na Australia da ke kasar Papua New Guinea.

Rikicin ya biyo bayan rahoton da ya fito ranar Lahadi cewa masu neman mafakar da dama sun tsere daga sansanin da ke tsibirin Manus.

Ministan harkokin shige da ficen Australia Scott Barrison ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici.

Sai dai ya ce babu wani sauyi da za a samu dangane da tsarin gwamnatin kasar na tantance masu neman mafaka a sansanonin da ke kasashen kudancin tekun Pacific.