'Yan Diffa sun koka da 'yan gudun hijirar Nigeria

Wasu 'yan gudun hijira
Image caption 'Yan Najeriya da dama sun tsere zuwa Diffa

A Jamhuriyar Nijar al'umomin yankin Diffa sun fara kokawa da wasu matsaloli dake tattare da kwararar 'yan gudun hijra daga arewa maso gabashin Nigeria zuwa garin.

Daruruwan 'yan gudun hijira ne suka tsere daga Najeriya sakamakon hare-haren da 'yan Kungiyar Boko Haram suke kaiwa.

Mazauna garin Diffan sun ce ba su san irin mutanen da suke rayuwa da su ba, ko da yake wasunsu na cewa hukumomi na tantance mutanen kafin a basu mafaka.

Ita kuma gwamnatin jahar ta Diffa cewa tayi ta dauki dukkanin matakan da suka dace domin kare al'umma.

Karin bayani