'Cin hanci da rashawa ya maida Ghana baya'

Shugaban Kasar Ghana Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gwamnatin Ghana ta bayyana cewa tana iyakacin kokarin kauda cin hanci

A shekarun baya bayan nan ana yi wa Ghana kallon kasar da ta ci gaba ta fuskar tattalin arziki da kuma demokaradiya a Africa.

To sai dai masu lura da al'amurra na ganin ta samu ci baya saboda zargin cin hanci da rashawa dake neman yi ma ta katutu.

Hakan kuwa ya biyo bayan wasu miliyoyin cedi da dalolin Amurka da ake zargin sun salwanta ne, bayan bada wasu kwangiloli ga wasu kamfanonin da ake zargin basu gudanarda ayyukan ba.

Yayinda gwamnatin Ghanan dai ke cewa tana iyakacin kokarinta na magance lamarin, wasu suna ganin abinda gwamnatin take yi bai isa ba.

Karin bayani