Sanata Isaiah Balat ya rasu

Hakkin mallakar hoto balat facebook
Image caption Margayi Sanata Isaiah Balat

Daya daga cikin fitattun 'yan siyasa a jihar Kaduna dake arewacin Nigeria, Sanata Isaiah Balat ya rasu.

Margayi Balat ya rasu sakamakon jinya a babban asibitin gwamnatin tarrayya a Abuja a ranar Talata.

Kwamishinan yada labarai na jihar Kaduna, Mr Ben Bako ya tabbatarwa BBC rasuwar Sanata Balat din.

Kafin rasuwarsa, Sanata Balat shi ne mai baiwa mataimakin Shugaban Nigeria shawara ta fannin ayyuka na musamman.

Ya taba rike mukamin karamin ministan ayyuka sannan ya yi dan majalisar dattijai daga 2003 zuwa 2007.