Libya: An baiwa 'yan majalisa wa'adi

Shugabannin sojin sa kai na Libya sun baiwa 'yan majalisar dokoki sa'o'i biyar na su yi murabus.

A cikin wata sanarwar da aka watsa ta talabijin wani kwamandan sojin sa kai na Al-Qaaqaa da ba a bayyana sunansa ba ya ce duk wani dan siyasar da ya ki mika mulki za a tsare shi.

Kakakin majalisar dokokin wucin gadi ta Libya ya shedawa yan majalisa cewar gargadin tamkar juyin mulki ne.

Tun farko a cikin watan nan 'yan siyasa sun kada kuri'ar tsawaita wa'adinsu, abinda ya haddasa suka mai yawa.

Sojin sa kan da suka bayar da wa'adin sun fito ne daga Zintan, kuma sun sha kalubalantar gwamnatin tarayya.