Ansaru Baytul Maqdis ta kai hari a Masar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Bom din ya hallaka mutane uku da jikkata wasu 10.

Kungiyar masu kishin Islama da ke kasar Masar, Ansaru Bayt al-Maqdis ta dauki alhakin harin bom da aka kai kan wata motar masu yawon bude ido a kusa da iyakar kasar da Isra'ila.

Tashin bom din ya hallaka wasu 'yan asalin kasar Korea biyu, da direban motar sannan kuma ya jikkata fiye da mutane 10.

A wata sanarwa da suka wallafa a shafin yanar gizo mai suna 'yan jihadi, kungiyar tace za ta ci gaba da kai hari wuraren da suka shafi tattalin arzikin Masar

Wannan dai shi ne hari na farko da masu kaifin kishin Islamar suka kai akan masu yawon bude ido, wanda hakan ke nuna yadda masu kaifin kishin Islamar suka sauya salon kai hare-harensu.

Karin bayani