Nigeria ta ce dakarunta na da makamai

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojojin Nigeria na yaki da kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin kasar.

Gwamnatin Nigeria ta musanta zargin da gwamnan jihar Borno Alhaji Kashim Shettima ya yi cewa sojojin kasar na da karancin makamai a yakin da su ke da mayakan Boko Haram.

Fadar shugaban kasar ta ce bai kamata gwamnan ya rika wadannan kalamai ba, saboda hakan ka iya kashewa sojojin gwiwa a yakin da su ke yi da 'yan Boko Haram din.

Ta ce sam gwamnan ba shi da masaniya ko kuma kwarewar da zai iya magana game da yakin da ake tabkawa a jiharsa.

Sai dai kuma fadar shugaban kasar ta ce sojojin ba sa rike manyan makamai saboda gudun illata farar hula kasancewar abokan fadansu 'yan yakin sunkuru ne da ke fake wa cikin al'umma.

Karin bayani