An kawar da cutar Kurkunu a Nijar

Image caption Nijar ta samu takaddar shaidar kauda kurkunu

Rahotanni daga jamhuriyar Nijar na cewa hukumar lafiya ta Majalisar dinkin duniya ta bayyana cewar an kawar da cutar kurkunu a kasar.

Kasar ta Nijar ta kasance daya daga cikin kasashe 21 a nahiyar Afrika da Asiya inda ake samun wannan cuta a baya.

Ministan lafiya na Nijar Malam Manu Agali ya shaidawa BBC cewa tuni aka baiwa Nijar takardar shaidar cewa babu cutar a Kasar baki daya

Kafin Nijar ta kaiga wannan matsayi dai wasu daga cikin matakan data dauka sun hada da bada rahotan duk cutar kurkunu da aka gani.

Buku da kari hukumomi sukan bada tukwuici ga duk wanda ya kawo irin wannan rahoto in ji ministan lafiyar.

Karin bayani