"Yan siysar Nijar ku zauna lafiya"

Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption An kai hari gidan shugaban majalisar dokokin Nijar, Alhaji Hamma Amadou.

Kungiyoyin addini a jamhuriyar Nijar na kira ga 'yan siyasa da su zauna lafiya da juna bayan harin da aka kai gidan shugaban majalisar dokoki, Alhaji Hamma Amadou.

Hadin gwiwar kungiyoyin addinin Islama na jamhuriyar Nijar sun fitar da sanarwar da ta nemi 'yan siyasar da su guji haddasa tashin hankali a fadin kasar.

Haka kuma kungiyoyin addinin Kirista a Damagaram sun yi makamancin wannan kira.

Rabaran Pasto Haruna Labbo na Damagaram ya bukaci 'yan siyasar da su kauce wa tada fitina saboda ta na iya ritsa wa da 'yan uwansu da iyalansu.

Karin bayani