Majalisa ta amince naddin ministoci 11

Hakkin mallakar hoto davidmark facebook
Image caption Shugaban Majalisar Dattijai Sanata David Mark

Majalisar dattijan Nigeria ta amince da sunayen mutane 11 don a nadasu a matsayin ministoci a kasar.

A zamanta na ranar Talata, majalisar ta baiwa Shugaba Jonathan damar nada mutanen a matsayin ministoci.

Wadanda aka amince dasu su ne Janar Aliyu Gusau mai ritaya (Zamfara), Sanata Musiliu Obanikoro (Lagos); da kuma Boni Haruna (Adamawa).

Sauran sun hada da Muhammad Wakil (Borno); Alhaji Abduljelili Oyewale Adesiyan (Osun); Ambasada Aminu Wali (Kano).

Sai kuma Akon Etim Eyakenyi (Akwa Ibom); Lawrencia Labaran Malam (Kaduna); Dr T. W. Danagogo (Rivers); Asabe Asmau Ahmed (Niger) da Dr. Khaliru Alhassan (Sokoto).

Sai dai ba a amince da nadin Hajiya Jamila Salik daga jihar Kano ba.

Karin bayani