An kasa cimma matsaya a rikicin Ukraine

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan sanda na kokarin kawar da masu zanga-zanga.

Bayan mafi munin tashin hankalin da aka gani a Ukraine tun bayan barkewar rikicin siyasa watanni uku da su ka wuce, daya daga cikin manyan jagororin 'yan adawa ya ce tattaunawa da shugaba Viktor Yanukovych ba ta tsinana komai ba.

Vitali Klitschko ya ce shugaban kasar ya bukace masu zanga-zangar adawa da gwamnati su janye daga tsakiyar birnin Kiev ba tare da sun gindaya wani sharadi ba.

A na dai cikin halin kiki-kaka a dandalin Indipendence na Kiev tsakanin masu zanga-zangar da 'yan sandan da ke kokarin fitar da su.

Masu zanga-zangar sun hada wuta ganga-ganga inda su ke kona tayoyi a cikin daren Laraba.

Akalla mutane 20 ciki har da 'yan sanda shida aka kashe a tarzomar, yayin da aka jikkata wasu da dama.

Karin bayani