Kulab din Fulham ya yi kora

Rene Meulensteen Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rene Meulensteen ya nuna cewa shi bai koru ba

Kulab din Fulham ya sallami tsohon Shugaban Kulab din Rene Meulensteen da kuma masu horar da 'yan wasan Ray Wilkins da kuma Alan Curbishley.

Kulab din Fulham ya maye gurbin Meulensteen a matsayin Shugaba da Felix Magath a ranar jumu'a.

To amma a cewar Meulensteen har yanzu kwanturaginsa da kulab din na nan daram.

Mutanen uku wadanda aka nada kan mukamansu watanni hudun da suka gabata zasu tafi ne tare da masu horar da 'yan wasa Mick Priest da kuma Jonathan Hill.