'Ana kawo tarnaki ga yaki da fyade a Nijar'

Image caption Matsalar fyade ga kananan yara na karuwa a Nijar

Wani Alkali a babban birnin Yamai dake aikin bincike kan fyade ya fuskanci wulakanci daga wata 'yar majalisar dokoki.

Hakan ya tunzura Alkalan Kasar ta Nijar suka fitar da wata sanarwa.

Su ma kungiyoyin kare hakkin mata da iyayen yara sun koka da abkuwar wannan lamari.

Matsalar cin zarafin 'ya'ya mata ta hanyar yi musu fyade na karuwa musamman a jahar Damagaram yanzu haka.

Rahotanin sun nuna cewa rufa -rufa da wasu iyayen keyi na kara karfafa gwiwar masu wannan aika- aika.

Karin bayani