An saka wa shugabannin Ukraine takunkumi

Image caption Wasu daga cikin wadanda suka rasu a Ukraine

Kungiyar Tarayyar Turai ta amince ta saka takunkumi a kan wadanda ta ce sune ke da alhakin tashin hankalin dake faruwa a Ukraine.

Kungiyar ta dauki wannnan matakin ne a birnin Brussels, bayan an kashe mutane da dama a Kiev, babban birnin kasar ta Ukraine a artabu mafi muni da aka taba yi, tun lokacin da aka fara zanga-zangar nuna kin jin gwamnati a cikin watan Nuwamba.

Catherine Ashton, ita ce Babbar jamiar dake kula da manufar harkokin wajen Tarayyar Turan, ta kuma ce ganin yadda al'ammura ke kara tabarbarewa a Ukraine, mun yanke shawarar daukan matakai na saka takunkumi, wanda zai hada da hana Ukraine sayo kayyakin da zaa iya amfani da su wajen takura ma abokan hammaya.

Wata tawagar ministoci uku na kungiyar sun shafe yinin yau a Ukarine din suna tattaunawa da bangarorin biyu, a wani yunkuri na samar da hanyoyion warware rikicin cikin ruwan sanyi.

Karin bayani