Ferguson ya shiga cikin Kochiyoyi

Everton Hakkin mallakar hoto All Sport
Image caption Ferguson ya hade da Everton a shekarar 1994

Tsohon dan wasan gaban Everton Duncan Ferguson zai shiga tawagar kochiyoyin erverton na dindindin.

Ferguson mai shekaru 42 a duniya ya kasance cikin jami’an kochiyoyin tun shekarar 2011.

Daga ranar Litinin zai hade da Manajan Kulab din Roberto Martinez.

Ferguson ya hade da Everton a shekarar 1994 tun farko a matsayin aro daga Rangers.

A shekarar 1998 kulab din Newcastle ya dauke shi a kwanturagin £8m kafin kudaden su koma £3.75m a shekarar 2000