Masu kashe kansu na karuwa a Nigeria

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption BBC ta samu rahotannin wadanda suka kashe kansu a Gombe, Bauchi da Taraba.

Adadin masu kashe kansu da kansu na karuwa a Nigeria musamman a arewacin kasar.

A baya bayan nan BBC Hausa ta ba da rahoton wadanda suka kashe kansu a jihohin Bauchi, Gombe, Taraba da ma sauran sassan kasar.

A cewar masana mafi yawan masu kashe kansu na yin haka ne saboda kuncin rayuwa ko kuma kasa cimma wasu bukatu.

Don haka su ka shawarci mahukuntan Nigeria da su samar da kayayyakin more rayuwa ta yadda 'yan kasar za su kubuta daga matsanancin halin da kan sa wasu su kashe kansu.