Darajar Naira ta fadi saboda dakatar da Sanusi

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption An samu daidaito lokacin mulkin Sanusi Lamido Sanusi

Darajar kudin Nigeria ta fadi kasa warwas sannan kuma an rufe kasuwar hada-hadar hannun jarin kasar, bayan da Shugaba Jonathan ya dakatar da gwamnan babban bankin kasar, Sanusi Lamido Sanusi.

Masana kan harkokin tattalin arziki sun ce darajar naira ta fadi idan aka kwantanta da dalar Amurka.

Sannan kuma tun bayan sanarwar fadar shugaban kasar, aka dakatar da harkoki a kasuwar hannun jari a Lagos.

Masu sharhi kan al'amuran kudi a kasar sun ce dakatar da Sanusi Lamdio Sanusi za ta yi mummunar tasiri a kan bangaren hada-hadar kudin Nigeria.

Gwamnan babban bankin ya zargi kamfanin man Nigeria NNPC da barnata kudin harajin danyen man fetur, abinda ya janyo takun sakarsa da Shugaban kasar, Goodluck Jonathan.

Karin bayani