Rikici a lardin 'yan Shi'a a Saudiyya

Image caption Sarki Abdullah na Saudiyya

Hukumomi a Saudiyya sun ce an kashe wasu mutane biyu da ake nema ruwa ajallo da kuma 'yan sanda biyu a rikici a lardin 'yan Shi'a dake gabashin kasar.

Hakan ya biyo bayan zanga-zangar kin jinin gwamnati da aka yi a lardin.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta ce an budewa 'yan sanda wuta ne lokacin da suka ziyarci lardin Awamiya don tsare mutanen biyu.

Wasu shafukan intanet masu alaka da 'yan shi'a sun ce daya daga cikin wadanda aka kashe sunansa Hussein Ali- al-Faraj wanda ya yi fice wajen daukar hotunan zanga-zanga.

Rikicin na zuwa ne kwana guda bayan da aka yankewa masu zanga-zanga bakwai hukuncin daurin kusan shekaru ashirin a kurkuku.

Karin bayani