Ukraine ta sasanta da 'yan adawa

Image caption Wuta na ci gaba da tashi a kewayen dandalin Independence na birnin Kiev.

Shugaban kasar Ukraine, Viktor Yanukovych ya amince da sulhuntawa da jagororin 'yan adawa bayan kwana biyu ana tata-burza tsakanin 'yan sandan kwantar da tarzoma da masu zanga-zangar adawa da gwamnati a babban birnin kasar, Kiev da wasu biranen.

Bayan tattaunawa da shugabannin 'yan adawar guda uku, Mr Yanukovych ya fitar da sanarwar cewa sun amince da tattaunawar da za ta kawo karshen zubar da jini.

Biyu daga cikin jagororin adawar, Vitali Klitschko da Arseniy Yatsenyuk sun ce shugaban kasar ya kuma ba da tabbacin ba za a kara kai farmaki kan sansanin masu zanga-zangar da ke birnin Kiev ba.

Wuta dai na ci gaba da ci a kewayen dandalin Independence na birnin Kiev inda masu zanga-zangar da 'yan sandan kwantar da tarzoma ke kallon-kallo da juna.

Akalla mutane 26 aka kashe tare da jiikkata daruruwa tun bayan barkewar hatsaniyar a ranar Talata.

Karin bayani