'Dakatar da Sanusi Lamido ya saba doka'

Image caption APC ta ce dakatar da gwamnan babban banki ya saba wa dokar Nigeria.

Babbar jam'iyyar adawa ta Nigeria, APC ta soki matakin da shugaban kasar Goodluck Jonathan ya dauka na dakatar da gwamnan Babban Bankin kasar, Sanusi Lamido Sanusi daga kan mukaminsa.

Mataimakin sakataren tsare tsare na jam'iyyar, Sanata Lawal Shuaibu ya ce matakin ya saba dokar da ta ce majalisar dattawa ce kadai za ta iya sauke gwamnan babban bankin kasar.

Ranar Alhamis ne dai gwamnatin Najeriyar ta sanar da dakatar da Malam Sanusi ne saboda " kashe kudi ba bisa ka'ida ba, da kuma sabawa ka'idojin aiki".

Tuni majalisar wakilan kasar ta zartar da kudirin kin amince wa da matakin da Shugaba Jonathan ya dauka na dakatar da gwamnan Babban Bankin.

Karin bayani