'Wasan Hutton a Aston villa yazo karshe'

Hutton yana wasa Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Aston villla na fuskantar matsalolin kudi

Da wuya dan wasan bayan Kulab din Aston Villa Alan Hutton ya sake taka wasa a kulab din saboda matsalolin kudi da kulab din ke fuskanta kamar yadda Manajan kulab din Paul Lambert ya bayyana.

Dan wasan mai shekaru 29 a duniya wanda ake biyansa £40,000 a mako kamar yadda rahotanni suka nuna, bai takawa Villa was aba tun watan Mayun shekarar 2012.

Da aka tambaye shi idan Hutton zai sake takawa Villa wasa, Lambert y ace “ Zai yi wuya” Ya san da haka.

Hutton wanda kwanturaginsa zai kare a shekarar 2015 ya tafi zuwa Nottinghma a matsayin aro a watan Disambar shekara 2012