Motoci masu amfani da lantarki a Bhutan

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Za a samar da tashoshin cajin motocin a daukacin Kasar.

Daular Himalayan ta Bhutan ta sanya hannu kan wata yarjejeniya tare da kamfanin kera motocin Japan na Nissan domin samar da motoci masu amfani da lantarki ga ayarin motocin gwamnati da kuma motocin haya.

Karkashin yarjejeniyar, Nissan zai samar da daruruwan motoci masu amfani da wutar lantarki da kuma samar da tashoshin caji a daukacin Kasar.

Bhutan na samar da hasken wutar lantarkin ta, ta hanyar amfani da ruwa, amma har yanzu tana dogaro ne da man fetur domin bukatun matuka motocin kasar.

Firayim Minista Tshering Tobgay ya ce yarjejeniyar zata taimakawa gwamnati burin da take da shi na son ganin ta daina fitar da hayaki mai gurbata yanayi.