Malamai sun haramta zuwa duniyar Mars

Hakkin mallakar hoto ISRO
Image caption Musulmi da dama a yankin Larabawa nada burin zuwa duniyar Mars

Wata kungiyar malaman addinin musulunci a Hadaddiyar Daular Larabawa ta fitar da wata fatwah na haramta tafiya zuwa duniyar Mars.

Malaman na jin cewa irin wannan balaguro nada hatsari ga rayuwa.

Kungiyar malaman addinin musuluncin dake a Abu Dhabi ta ce irin wannan tafiya zuwa duniyar Mars daidai yake da mutum ya kashe kansa, saboda ba a san yadda mutane zasu rayu a can ba.

An fitar da Fatawar bayan rahotannin dake cewa musulmi da dama daga Kasashen larabawa sun sanya hannun yin wannan tafiya zuwa duniyar wata a shekarar 2024 bayanda wani kamfani ya tallata.