Taron adu'oi na Komla Dumor

Komla Dumor
Image caption Komla Dumor

An sama taron adu'oin jana'izar mai gabatar da shirye -shirye na BBC Komla Dumor a kasar haihuwarsa watau Ghana .

Marigayin ya mutu ne a watan daya gabata yana mai shekaru 41 a duniya.

Komla Dumor shahararen mai gabatar da shirye- shirye ne a gidajen rediyo a kasar Ghana kafin ya koma BBC da aiki shekaru 7 da suka wuce.

Tsohon shugaban kasar Ghana Jerry Rawlings ya ce an yi babban rashi musaman idan an yi la'akari da cewa shi mutum ne mai kare mutunci jama'a.

An yi wake-wake a cocin katolika dake Accra inda da za'a shafe kwanaki uku ana taron adu'oi.

Haka kuma 'yan kasar Ghana da suka fito daga sassan kasar dabam -dabam sun rika wuce akwatin gawarsa domin su yi masa ban kwana.

Idan an jima a yau za'a cigaba da taron adu'oi a fadar shugaban kasa