Za a fara jana'izar Komla Dumor

Image caption Komla Dumor ya yi mutuwar fuj'a ya na da shekaru 41.

A ranar Juma'ar nan ne za a fara jana'izar mai gabatar da shirye-shiryen BBC, Komla Dumor - wanda ya yi mutuwar fuju'a a watan jiya ya na da shekaru 41- a kasarsa ta haihuwa, Ghana.

Kamar yadda al'adar Ghana ta ke, za a gudanar da jana'izar ne tsawon kwanaki uku.

Za a fara ne da addu'o'i a cocin Roman Katolika na birnin Accra inda za a kwantar da gawarsa domin ban kwana da ita.

Mutuwar Komla Dumor ta haddasa makoki a sassa dabam-daban na duniya kuma shugaban kasar Ghana ya ce kasar ta yi rashin daya daga cikin manyan jakadunta.

Karin bayani