Magath: Ba zan yi sassauci ba

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Magath ya ce babu abinda zai sa ya canza horon sa duk da ana kiransa mai kama karya

Shugaban Kulab din Fulham Felix Magath ya ce ba zai canza tsatsauran salon Shugabancin sa ba a Fulham yana mai cewa 'babu wanda ya mutu daga ladabtarwa'.

An ruwaito cewa tsohon dan was an kulab din Bachirou Salou ya bayyana Magath mai shekaru 60 a duniya a matsayin ‘mai kama karya na karshe a Turai’.

Amma Magath ya ce: “me yasa zan canza yadda nake horo? Nine mai horar da ‘yan wasan da yafi kowa nasara a Jamus.

Since arriving at Craven Cottage, Magath has already called the Fulham squad in for extra training sessions.

Magath dai ya kira ‘yan wasan Fulham din zuwa wani atisaye na karin lokaci tun lokacin daya zo Kulab din.