Robert Mugabe ya cika shekaru 90

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Mugabe na shan suka daga kasashen Turai

Shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe ya cika shekaru tasa'in a duniya.

Mista Mugabe, wanda shine ya fi tsufa daga cikin shugabannin Afirka, yana can kwance a wani asibiti a Singapore, inda ake masa magani.

Gwamnatin Zimbabwe dai ta dage kan cewa, ana yi masa aiki ne a ido, kamar yadda aka saba, kuma zai koma gida, ranar Lahadi, domin bikin cika shekarunsa tasa'in.

To sai dai har yanzu a Zimbabwe akwai shakku game da koshin lafiyar shugaban.

Shekaru talatin da hudu kenan da Robert Mugabe ke kan karagar mulki - watau tun lokacin da Zimbabwe ta sami 'yancin kai daga Birtaniya.

Karin bayani