'A soke ganawar Dalai Lama da Obama'

Hakkin mallakar hoto White House
Image caption Mr Obama ya gana da Dalai Lama a shekarar 2010.

China ta shawarci Amurka da ta soke ganawar da aka shirya yi tsakanin shugaba Obama da shugaban addini na Tibet mai gudun hijira, Dalai Lama, inda ta yi gargadin cewa ganawar za ta bata dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.

A ranar Juma'a ne dai ake sa ran Mr Obama zai gana da Dalai Lama din a fadar White House.

Kakakin ma'aikatar hulda da kasashen waje ta China ta ce ganawar katsalandan ne cikin al'amuran cikin gida na Chinan.

Jam'ian Amurka sun ce tattaunawar za ta mai da hankali ne kan batun kare hakkin bil'adama a yankunan Tibet na kasar China.

Karin bayani