Rooney ya sabunta kwangilarsa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An yi takun saka tsakanin Rooney da tsohon kocin United

Dan kwallon Manchester United Wayne Rooney ya amince da yarjejeniyar shekaru biyar da rabi a kan fan dubu 300 kowanne mako don ci gaba da taka leda a Old Trafford.

Dan shekaru 28, dan wasan Ingilan zai ci gaba da kasancewa da kungiyar har zuwa watan Yunin 2019.

Tsohuwar yarjejeniyarsa da United za ta kare ne a badi, inda aka bashi fan dubu 250 kowanne mako.

Rooney ya hade da United daga Everton a watan Agustan 2004, kuma sauran kwallaye 42 ya kamo yawan kwallayen da Bobby Charlton ya zura a United.

Tsohon dan kwallon Everton din ya bugawa United wasanni 430 inda ya zura kwallaye 208.

Karin bayani