An kai hari fadar Shugaban Kasar Somalia

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan bindiga sun so shiga fadar Shugaban Kasar Somalia

Masu kaifin kishin Islama a Somalia sun kai hari fadar Shugaban Kasa a babban birnin Mogadishu na Somalia.

Rahotanni sun ce 'yan bindigar sun soma kai farmakin ne tare da tada bom na mota a mashigar fadar Shugaban Kasar, sannan sukai kokarin kutsa kai ciki ta karfi.

An ji karar fashewar abubuwa sau biyu.

Wano shafin intanet da ake alakantawa da kungiyar Al-Shabab (Somali Memo) ne ya bada labarin harin dake gudana cikin fadar Shugaban Kasar.

Sai dai wakilin Majalisar dinkin duniya na musamman a Somalia Nick Kay ya ce Shugaban Kasar Somalia ya fada masa cewa bai samu koda kwarzane ba, kuma harin bai samu nasara ba.

Kungiyar Al Shabab dai na yakin sari ka noke ne a Somalia bayan da aka fatattake ta a shekarar 2011