Rikicin kasar Sudan ta Kudu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan gudun hijira a Sudan ta Kudu

Wani rahoto na wucin gadi da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar akan rikicin Sudan ta Kudu ya ce dakarun gwamnati da kuma 'yan tawaye dukanninsu sun toye hakkin bil'adama.

Rahoton ya kuma ce rikicin ya fi shafar fararen hula.

Rahoton ya ce dukannin bangarorin sun aikata miyagun laifuka ciki harda fyade da kashe-kashen mutane masu dimbin yawa da kuma azabtarwa bisa kabilar da mutum ya fito.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce dakarun gwamnati dake yi wa shugaba Salvir Kiir biyaya wanda ya fito daga kabilar Dinka sun kashe 'yan kabilar Nuer a Juba babban birnin kasar a farkon rikicin.

Haka kuma rahoton ya ce ya gano cewa matasa kabilar Nuer sun kashe 'yan kabilar Dinka a garin Malakal