Amurka ta yi maraba da yarjejeniyar Ukraine

Barak Obama Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Barak Obama

'Fadar Amurka ta White House ta yi maraba da yarjejeniyar da aka kulla tsakanin shugaba Viktor Yanukovych na Ukraine da shugabannin 'yan adawa domin kawo karshen rikicin siyasar kasar.

Shugaba Obama ya yi magana da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin ta wayar tarho domin su tattauna akan kasar ta Ukraine da kuma sauran batutuwa da suka shafi duniya.

Shugabannin sun ce akwai bukatar ganin cewa alamura sun daidaita musaman tattalin arzikin kasar tare da aiwatar da sauye sauye da kuma bukatar ganin cewa bangarorin biyu sun yi hankuri .

Karkashin yarjejeniyar da aka cimma za a kafa wata gwamnatin wucin gadi kuma za a gudanar da zabuka a watan disemba na shekarar da mu ke ciki.

Karin bayani