Maduro zai kori CNN daga Venezuela

Nicolas Maduro Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'CNN ta watsa rahotannin zanga zanga a Venezuela'

Shugaban Kasar venezuela Nicolas Maduro ya yi barazanar korar Tashar watsa labaran Amurka ta CNN daga Kasar game da rahotannin data watsa na zanga zangar da aka gudanar a Kasar a baya- bayan nan.

Mr. Maduro ya soki CNN da watsa farfagandar yaki akan Kasar sa.

Shugaban Ya kuma ce za a kori tashar idan har bata canza yadda take bada rahotanni ba.

Wata mai magana da yawun CNN ya shaidawa BBC cewa a yanzu ba zasu ce komai ba ta hanyar maida martani.