Yau ake bikin ranar haihuwar Mugabe

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Bikin ranar haihuwar Mugaben shi ne na casa'in

A zimbabwe yau ne ake bikin zagayowar ranar haihuwar shugaban kasar Robert Mugabe.

An yi kiyasin bikin zai ci dala miliyan daya, wanda kuma za a yi a wani babban filin wasa da ke dan karamin garin Marondera da ke gabashin babban birnin kasar Harare.

Wasu na suka kan yawan kudin da za a kashe a bikin saboda yadda tattalin arzikin kasar ke koma-baya da kuma matsalar rashin aikin yi.

Ranar Juma'a ce ainihin ranar haihuwar shugaban amma aka dage bikin har zuwa Lahadin nan saboda shugaban yana Singapore inda aka yi masa aikin ido.