Nakiya ta fashe a garin Iferouane na Nijar

Hakkin mallakar hoto

A Jamhuriyar Nijar wata nakiya ta tashi da wata mota a garin Iferouane dan lokaci kadan kafin bude bikin festival de l'Air da ake yi a garin a kowace shekara, don nuna cewa an sami zaman lafiya a yankin da yayi fama da tawaye a shekarun baya.

Mutum daya daga cikin wadanda ke cikin motar ya jikata kuma an garzaya da shi a asibiti.

Ya zuwa yanzu dai ba a kai ga tantance ko su wane ne suka dasa nakiyar ba.