Matsalar rashin gurfanar da mutane da ake tuhuma gaban kotu a Najeriya

Nigeria prisons Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani gidan yari a Najeriya

A Najeriya, wani abu da ke kara haifar da matsalar cunkoso a gidajen yarin kasar, shi ne yadda akan kai mutanen da ake zarginsu da aikata miyagun laifuka,a tsaresu na lokaci mai tsawo ba tare da an gurfanar da su gaban kotu ba.

A jihar Enugu kadai ana da mutane kusan dari takwas da ke cikin irin wannan hali a gidajen yari uku.

Bisa la'akari da haka ne wata kungiya mai zaman kanta da ke karkashin cocin darikar Katolika, mai suna CAPIO ta shigar da kara a wata babbar kotun tarayya da ke Enugun, tana neman a san na yi da wadannan mutane.

Kungiyar ta ce yin haka ya sabawa dokokin kundin tsarin mulkin kasar