An kashe sojojin Afghanistan 20

Taswirar Afghanistan
Image caption Taswirar Afghanistan

An hallaka sojojin Afghanistan 20 a lardin Kunar na gabashin kasar, a abinda ake ganin shine hari mafi muni da aka kaiwa dakarun tsaron kasar a cikin shekara guda.

'Yan bindiga sun yi wa sojojin Afghanistan din kwantan bauna ne a wani wurin bincike na kan hanya.

Ma'aikatar tsaron Afghanistan ta ce daruruwan 'yan fafutuka, baki da na cikin gida ne suka kai harin a daren jiya.

Daya daga cikin maharan ya rasa ransa.

An cigaba da gumurzun har ya zuwa safiyar yau, yayin da 'yan bindigar ke ta bude wuta daga tsaunukan da suka ja daga.

Shugaban kasar, Hamid Karzai, yayi Allah wadai da asarar rayukan da aka samu, kuma ya soke ziyarar da ya shirya kaiwa Sri Lanka.

Yayi kira ga makwabciyar kasar Pakistan da ta kawar da abinda ya kira: tuddan mun tsirar 'yan ta'adda a kasar, wadanda ya ce suna taimakawa wajen kai hare-hare a kan iyakar.

A cikin sakon email da ya aiko wa BBC, wani mai magana da yawun 'yan Taliban ya ce sune suka kai harin, kuma sun yi garkuwa da sojoji bakwai na gwamnatin Afghanistan.