Amurka ta yi tur da hare haren Boko Haram

Yaki da Boko Haram a Najeriya Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Yaki da Boko Haram a Najeriya

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya yi Alla wadai da hare haren baya baya nan da 'yan kungiyar da ake kira boko haram ke kaiwa a Najeriya.

A cikin wata sanarwa da aka aikewa manema labaru Mr Kerry ya ce rikici ne mai tada hankali kuma ba dai dai bane kuma duniya ba za ta amince da shi ba .

Sakataren harkokin wajen Amurka ya yi alkawarin cewa kasarsa za ta ci gaba da marawa Najeriya baya wajen yaki da kungiyar wadda gwamnati Amurka ta bayana a matsayin 'yan ta'ada.

Mayakan kungiyar ta boko haram sun kashe mutane fiye da dari a garin Bama dake jihar Borno ranar larabar da gabata da kuma mutane fiye da dari a garin Izge ranar lahadin data gabata.

Haka kuma wasu'yan bindigar da ake zaton 'yan Boko Haram ne sun kai sabon hari a garin Izge na jihar Borno a daren Asabar.

Mazauna garin sun shaida wa BBC cewa maharan sun yi ta yin luguden wuta har sai da su ka kone garin kurmus.

Rahotanni sun ce akalla mutane hudu sun hallaka kuma a yanzu babu kowa a garin.

Karin bayani