An sace wani dattijo a jihar Bayelsa

Wasu jami'an tsaron Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sace mutane domin neman kudin fansa ta zama ruwan dare a kudancin Najeriya

Rahotanni daga Najeriya, sun ce rundunar 'yan sandan jihar Bayelsa ta kama wasu mutane biyu wadanda ake zargin sun sace wani dattijo a garin Utoke na jihar Bayelsa.

Sai dai har yanzu ba a sami wani cikakken bayani game da inda aka tafi da dattijon ba, wanda wasu bayanai ke cewa uban goyo ko mariki ne na shugaban kasa, Dokta Goodluck Jonathan.

Ko da yake babu wata majiya mai tushe da ta tabbatar da dangantakar dattijon da shugaban kasa.

Sace mutane don neman a biya kudin fansa kafin a sako su dai wata gagarumar matsalar tsaro ce da ke addabar jama'ar Najeriya, musamman ma a kudancin kasar.

Karin bayani