Damisa ta razana mutane a India

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption An rufe makarantu da kasuwanni saboda Damisar

Wata Damisa ta janyo rudani a jahar Uttar Pradesh dake arewacin India bayan data bazama cikin wani asibiti da cikin gidan kallo da kuma wani gini.

Jami'ai sun ce an kasa kama Damisar duk kuwa da kokarin da aka yi na ganin an yi hakan.

Hotunan da aka dauka sun nuna yadda Damisar ta dinga addabar jama'a.

Akalla mutum guda ya jikkata.

Rundunar soji ta killace yankin da aka ga Damisar, sannan an rufe makarantu da kwalejoji da kasuwanni a ranar.