Abubuwa tara game da Mugabe

Image caption Robert Mugabe

Robert Mugabe ya cika shekaru 90 a duniya inda aka yi bukukuwa a kasar Zimbabwe saboda tsawon ran shugaban kasar.

An haifeshi a kauyen Kutama dake kudu maso yammacin babban birnin kasar Harare, kuma ya yi karatu a marantar Jesuit kafin ya zaman malamin makaranta.

Daga bisani ya shiga kungiyar gwagwarmayar kwatar 'yanci inda ya shafe shekary 11 a kurkuku kafin zamowa shugaban kasar Zimbabwe na farko a shekarar 1980.

Ga abubuwa tara da watakila baku sani ba a kan sa:

1) Atisaye da cin abincin gargajiya:

" Na kanyi ciwo idan ban motsa jiki ba," Mugabe ya fadi haka shekaru uku da suka wuce. Ya kanyi bacci kadan ya mike tun karfe 4 na asuba ya motsa jiki duk safiya har zuwa karfe 5. Sannan wata majiya tace yana sauraron BBC.

Wani sirrin tsawon ransa shi ne yawan cin 'sadza' abincin gargajiyar Zimbabwe da ake yi da masara. Kuma bai shan sigari amma ya kan sha barasa lokacin liyafar cin abincin dare.

2) Tsoho mai ran karfe

Duk da yawan jita-jitar kan rashin lafiyarsa- shafin kwamata bayanai na Wikileaks ya ce Mugabe na fama da ciwon cancer. Amma an tabbatar yana fama da ciwon amosanin ido kuma an yi masa tiyata. " Na mutu sau da yawa amma kuma na sake farfadowa," ya fadi hakan lokacin yanada shekaru 88. Ko da yake iyayensa kiristoci ne amma shi ya bayyana cewar baya bin addinni sau da kafa.

3) Mai son wasan Kruket

Hakkin mallakar hoto Reuters

Ya dade a matsayin sa na mai goyon bayan wasan kruket. Kuma shi ne uban kungiyar Kruket ta Zimbabwe kuma fadarsa tana daura da cibiyar wasanni ta Harare, abinda ke bashi damar sa'ido a kan wasannin kruket.

4) Baya daukar kaddara

Yana karamin yaro, Robert Mugabe yana buga wasan tennis, kamar yadda wani malami a makarantar Firamare da ya yi, ya bayyana. Kuma idan aka doke shi sai ya yar da abin buga wasan tennis din. Da bakinsa ya bayyana cewar yana goyon bayan Chelsea da Barcelona ne. "Idan ina kallon kwallo banason kowa ya dame ni".

5) Ya fi son Cliff Richard a kan Bob Marley

Tsohon dan siyasar Zimbabwe Edgar Tekere ya shaidawa BBC cewar lokacin da ake kokarin shirya bukin samun 'yancin kai a Zimbabwe a shekarar 1980, Mr Mugabe bai nuna sha'awar a gayyaci Bob Marley ba. Idan ya ce yafi son mawakin Birtaniya Cliff Richard. Wasu kuma sun bayyana cewar Mr Mugabe ya nemi a gayyaci Jimmy Cliff na Jamaica don ya cafe a wasu bukukuwar da aka yi a shekarun 1980.

6) Sha'awar rigar kwat

Mugabe ya kasance mai sha'awar rigar kwat ne a duka lokacin bukukuwa kafin daga bisani ya soma saka rigunan dake da launi iri-iri. Wani tela dan Zimbabwe mai suna Khalil 'Solly' Parbhoo ya ce " Har yanzu yana shiga kamar bature. Heidi Holland ko cewa ya yi "Ana kawo masa kwat ne daga London ko kuma daga Malaysia."

7) Jinjinawa Kwame Nkrumah

Mr Mugabe ya soma sha'awar siyasa a lokacin da yake Ghana a matsayin malamin makaranta inda ya hadu da matarsa ta farko Sally Hayfron. A cewarsa ya samu kwarin gwiwa ne daga wajen Kwame Nkrumah wato Firaministan Ghana na farko a shekarar 1957, wajen shiga gwagwarmayar kwatarwa Zimbabwe 'yanci.

Kuma daga komawarsa gida daga Ghana sai ya soma bayyanawa jama'a bukatar yin koyi da akidun Nkrumah na kwatar 'yancin bakar fata.

8) Takardun digiri da dama

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kwameh Nkurma na Ghana

Mr Mugabe yana da takardun shaidar karatun digiri har bakwai, tun bayan digirinsa na farko a jami'ar Fort Hare taa Afrika ta Kudu inda Nelson Mandela ya yi karatu. Ya samu digiri har biyu lokacin yana zaman kaso. Sai dai sakamakon irin matakan da ya dauka a kan fararen fata, an kwace masa wasu daga cikin lambobin yabon da aka bashi, ciki hadda lambar yabon da Sarauniya Elizabeth na Ingila ta kwace saboda laifin taka hakkin bil 'adama.

9) Matarsa ta haihu yana da shekaru 73

Yana da 'ya'ya uku tare matarsa ta biyu Grace Marufu wato tsohuwar sakatariyarsa. An haifar masa diyya na uku Chatunga a shekarar 1997, shekara guda bayan aurensu. Dan sa na farko Nhamodzenyika, ya rasu a Ghana yanada shekaru uku sakamakon ciwon zazzabin cizon sauro. Mr Mugabe wanda lokacin yana zaman kurkuku a Zimbabwe an hanashi zuwa jana'izar dan sa a Accra.

Karin bayani