Cutar Polio ta bulla a Amurka

Image caption Likitoci sun ce ba sa fargabar cutar za ta zama annoba

Kusan mutane ashirin ne suka kamu da wata cuta da ke kama da ta Polio wato shan'inna a cikin watanni 18 da suka gabata a California ta Amurka.

Cutar wadda alamunta suka kama daga rashin motsawar yatsa sosai zuwa tsananin kasala a kafafu da hannaye galibi tana shafar yara ne.

Likitoci sun jaddada cewa, da alamu cutar bakuwa ce amma kuma sun ce ba sa tsammanin za ta bazu sosai.

Wakilin BBC a fannin lafiya ya ce da alamu kwayar cutar dangi ce ta kwayar cutar polio da ake kira enterovirus-68.