'Za mu inganta yaki da 'yan Boko Haram'

Hakkin mallakar hoto Getty

Shugaba Goodluck Jonathan na Nigeria ya ce za a inganta yakin da ake yi da 'yan kungiyar da ake kira Boko Haram , kuma ya yi alkawarin samar da karin kariya a wuraren da tashin hankalin ya fi kamari.

Shugaba Jontahan ya bayyana haka ne yayin wata hira da 'yan jarida a ranar litinin.

Mr Jonathan ya maida martani ne akan sukar baya bayanan da ake yiwa gwamnatinsa kan gazawar da ake zargin sojin kasar sun yi wajen kare aukuwar hare- haren da 'yan kungiyar ta Boko Haram suke yawan kaiwa, da kuma rashin tasirin dokar ta baci da aka kafa a jihohin uku dake gabashin kasar.

Gwamnan jihar Borno Kashin Shetimma a baya bayanan shi ne ya bayyana cewa mayakan kungiyar Boko Haram sun fi sojojin kasar kayan yaki masu inganci da kuma kwarin gwuiwa .

Sai dai fadar Shugaban Najeriyar ta musanta wannan zargi.

Mutane fiye da da dari biyu aka kashe a makon da ya gabata a jihar Bornon

"Idan muka janye sojojinmu daga Borno"....

Shugaban Najeriyar ya kuma kalubalanci kalaman Gwamnan Borno na gazawar da yake zargin anyi wajen shawo kan rikicin 'yan kungiyar Boko Haram a jihar sa.

Dr Goodluck Jonathan ya ce "idan har gwamnati ta janye sojojinta daga Borno zamu ga ko Gwamna Shettima zai iya zaman gidan gwamnati".

Shugaba Jonathan ya kuma bayyana rashin jin dadinsa ga kalaman Gwamnan jihar Bornon.

"Har yanzu Sanusi ne Gwamnan Babban Banki"

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sanusi Lamido

Tattaunawar ta kuma tabo batun dakatar da gwamnan babban bankin kasar CBN, Malam Sanusi Lamido Sanusi, inda ya ce, ba cire shi ya yi ba, an dakatar da shi ne kawai.

Shugaba Goodluck Jonathan ya ce, a saninsa har yanzu Malam Sanusi shi ne gwamnan babban bankin Nigeria, amma an dakatar da shi ne domin duba wasu abubuwa.

'Muna so ne a yi bincike a kan abubuwa da suka taso na zargi dangane da babban bankin Nigeria' inji Shugaba Jonathan.