Wani matashi ya kashe mahaifinsa a Sokoto

Hakkin mallakar hoto Aliyu
Image caption Babban sfeto Janar na 'yan sanda Nigeria

'Yan sanda a jihar Sakkwaton Nigeria sun tsare da wani matashi da ake zarginsa da kashe mahaifinsa.

Makwabtan mamacin sun shaida wa BBC cewa wanda ake zargin, ya kashe mahaifin nasa ne ta hanyar sara da adda sa'annan ya binne shi a wani wuri a cikin gidansa a daren ranar Lahadi.

Kakakin rundunar 'yan sanda jihar Sokoto, DSP Almustapha Sani ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya bayyana cewar sun damke matashin da ake zargi da wannan aika-aikar.

Mamacin wato Malami Aliyu wanda ake kira Altine dan shekaru kimanin 55 ya gamu da ajalinsa ne da tsakar daren sa'adda dan nasa da ake zargi da kashe shi ya afka masa da sara da adda a yayin da ya ke sallah a gidansa dake unguwar Kofar Marke.

A lokacin da wakilin BBC ya ziyarci Caji Ofis na dadin kowa inda ake tsare da wanda ake zargin, ya tarar ana kokarin jana'izar mamacin.

Kawo yanzu ba'a san dalilan da suka sanya matashin kashe mahaifinsa ba.

Karin bayani