Amurka za ta ba Ukraine tallafi

Masu zanga-zanga a Ukraine Hakkin mallakar hoto g
Image caption Masu zanga-zanga a Ukraine

Amurka ta ce a shirye take ta taimakawa kasar Ukraine da kudi domin tattalin arzikin kasar ya inganta.

Kakakin fadar White House ya ce tallaffin zai taimakwa kasar wajen aiwatar da sauye sauye tare kuma da zuba jari a tsarin kiwon lafiya da kuma ilimi.

Itama Faransa ta ce shugaba Francoise Hollande ya jadada muhimanci mika mulki cikin kwanciyar hankali a kasar ta Ukraine.

Shugaban Faransa ya bayana haka ne a tattaunawar da suka yi da fira ministan Rasha Vladimir Putin ta wayar tarho.

Shugabbanin biyu sun yi magana da juna ne yayinda miministar harkokin wajen Turai Catherine Ashton ke Keiv domin su tattauna akan yadda za'a taimkawa sabbin shugabbanin kasar ta fuskar kudi da kuma siyasa.

Rasha ta yi suka mafi kaushi ya zuwa yanzu dangane da hambarar da shugaba Yanukovych a Ukraine, inda ta kira hakan a matsayin wata barazana ga al'ummar Rashan da kuma muradunsu.

Karin bayani