Amurka za ta rage yawan sojojinta

Chuck Hagel Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Chuck Hagel

Sakataren tsaron Amurka ,Chuck Hagel, ya gabatar da shawarar zaftare yawan sojojin Amurkan , abin da zai sa rundunar sojin kasar ta zama mafi karancin soji tun yakin duniya na biyu.

A wani jawabi da ya gabatar a hedikwatar tsaron kasar, Mr Hagel, ya ba da shawarar rage yawan sojojin Amurkan ta yadda ba za su wuce sama da dubu 450 ba.

Ya kuma ce za a rufe wasu sansanonin dakarun Amurkan tare kuma da rage jiragen yakin kasar na sama da na ruwa

Mr Hagel ya ce, saboda abubuwa uku ne suka dau wanana mataki, me fanni hudu da suke son sun yi amfani da shi don zamanantar da rundunar sojin Amurkan.

Ya kuma ce tun bayan yakin Iraqi da Afghanistan ba sa bukatar tarin dakaru da zasu yi wani fada.