Fanareti: Ingila tana shiri

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption England ta soma shirin gasar cin kofin duniya a Brazil

Mai horar da ‘yan wasan England Roy Hodgson zai yi amfani da masana kan halayyar dan Adam wajen bugun fenareti.

Manajan Ingilan Roy Hodgson zai duba yiwuwar amfani da masana halayyar dan Adam a gasar cin kofin duniyar a Brazil domin tabbatar da cewa ‘yan wasa sun shirya sosai ga bugun fenariti.

Hodgson ya ce muna da wasu ‘yan wasa da suke da kwarin gwiwa wajen iya bugun fenariti amma wasu basu da wannan kwarin gwiwar.

Ya danganta da yadda zaka same su. Muna bukatar mu san yadda suke da irin shirinsu

Mai horar da ‘yan wasan ya yi imanin cewa ana bukatar kwararru kan halayyar dan adam wadanda zasu iya taimakawa wajen kwantarwa da ‘yan wasa hankali idan aka zo bugun fenariti