John Mahama ya yi wa 'yan kasar jawabi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ghana na fuskantar karancin wuta da kuma ruwan sha

A kasar Ghana yau ne shugaban kasar wato John Mahama ya gabatar da jawabinsa ga al'umman kasar kan halin da kasar take ciki.

A cikin jawabin nasa shugaban kasar ya tabo abubuwa kamar tattalin arzikin kasar da makamashi da kuma ruwa da cin hanci da rashawa da kuma habbaka masana'antun kasar.

Ghana dai na fuskantar karancin wutar lantarki da kuma ruwan sha yanzu haka.