Mace-macen yara na karuwa

Hakkin mallakar hoto Other
Image caption "A Afrika lamarin mutuwar yaran ya fi muni a Njeriya"

Kungiyar agaji ta Save the Children ta ce duk da irin nasarar da ta cimma a kokarinta na kawo karshen yawan mace macen kananan yara, har yanzu kimanin yara miliyan guda ne ke mutuwa a duk shekara.

A cewar wani sabon rahoton kungiyar, yawan mace macen kanana yara tamkar wani abin kunya ne ga manyan kasashen duniya.

Rahoton ya ce a duk shekara jarirai miliyan daya ne ke mutuwa a duniya a ranar da aka haife su.

Rahoton ya ce a Afrika lamarin mutuwar yaran ya fi muni a Njeriya, wacce kuma ita ce ta biyu a duniya bayan India, yayin da kuma kasar take ta uku a wajen yin bari bayan Pakistan da Bangladesh.

Kungiyar ta ce mafi yawancin matsalolin dai na faruwa ne saboda matsalolin da mata masu juna biyu ke gamuwa da su har zuwa lokacin haihuwa.